9 Janairu 2020 - 06:58
Al Huts: Za Mu Marawa Iran Baya A Fadan Da Suke Da Amurka

Sayyid Abdulmalik Al Hutsis y ace za su marawa kasashen Iran, Lebanon, Iraki, Syria da palasdinu baya da suke fuskantar barazanar daga Amruka.

Taskar watsa labarai ta Ahlul-Baiti{a.s}ABNA24- ta rawaito,  Sayyid Abdulmalik Al Hutsis a cikin jawabinsa na  bikin shekara-shekara na ranar shahidai, inda ya ke  cewa; Bikin na shekarar bana ya zo ne a daidai lokacin da  abubuwa masu muhimmanci su ke faruwa da raunana a duniya za su amfana da su.

Da ya juya akan  Magana  shahadar Qasim Suleimani da Abu Mahdi al-Muhandis, wadanda Amurka ta yi wa kisan gilla, Sayyid Abdulmalik al-Hutsis ya ce; Harin da Amurka ta kai wanda ya yi sanadiyyar shahadar musulmi biyu ta’addanci ne.